Colossians 4

1Ku iyayengiji, ku ba bayinku abin ke daidai ya kuma dace garesu. Kun sani cewa ku ma, kuna da Ubangiji a sama.

2Ku cigaba da himmantuwa ga yin addu’a. Ku zauna a fadake cikin addu’a da godiya. 3Ku yi addu’a tare domin mu kuma, domin Allah ya bude kofa domin kalmar, a fadi asirin gaskiyar Almasihu. Don wannan ne nake cikin sarka. 4Ku yi addu’a domin in iya fadinsa daidai, yadda yakamata in fada.

5Ku yi tafiya da hikima game da wadanda suke a waje, ku yi amfani da lokaci. 6Bari maganarku ko yaushe ta zama ta alheri. Bari ta zama da dadin ji domin ku san yadda za ku amsa wa kowanne mutum.

7Game da abubuwan da nake ciki, Tikikus zai sanar maku da su. Shi kaunataccen dan’uwa, amintaccen bawa, shi abokin barantaka na ne a cikin Ubangiji. 8Na aike shi wurinku don wannan, domin ku iya sanin halin da muke ciki, don kuma ya karfafa zukatanku. 9Na aike shi tare da Onisimus, amintacce da kuma kaunataccen dan’uwa, wanda daya ne daga cikin ku. Za su gaya maku duk abin da ya faru anan.

10Aristarkus, abokin sarka na, yana gaishe ku da Markus, dan’uwan Barnaba (wanda a kansa ne kuka sami umarni; in yazo, ku karbe shi), 11da kuma Yesu wanda ake kira Yustus. Wadannan ne kadai daga cikin masu kaciya abokan aiki na domin mulkin Allah. Sun zama ta’aziya a gare ni.

12Abafaras na gaishe ku. Shi daya daga cikinku ne kuma bawan Almasihu Yesu ne. Kullum yana maku addu’a da himma, don ku tsaya cikakku da hakikancewa a cikin nufin Allah. 13Gama ina shaidarsa a kan ya yi aiki da himma domin ku, domin wadanda ke Lawudikiya, da na Hirafolis. 14Luka kaunataccen likita da Dimas suna gaishe ku.

15Ku gai da ‘yan’uwa dake a Lawudikiya, da Nimfa da ikilisiyar da ke cikin gidanta. 16Lokacin da aka karanta wannan wasika a tsakanin ku, sai a karanta ta kuma a cikin ikilisiyar Lawudikiya, ku kuma tabbata kun karanta wasika daga Lawudikiya. 17Ku gaya wa Arkibas, “Mai da hankali ga hidimar da ka karba cikin Ubangiji, don ka cika shi.”

18Wannan gaisuwa da hannu na ne - Bulus. Ku tuna da sarka na. Alheri ya tabbata a gare ku.

Copyright information for HauULB